Hukumomin Najeriya sun bayyana cewa, nan da kankanin lokaci ne kasar za ta yi hannun riga da matsalar tattalin arzikin da take fama da ita.
Shugaban babban bankin kasar, Godwin Emefile da ministan kasafi da tsare-tasre, Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Ministar kudi, Kemi Adeosun suka bayyana haka.
Gwamnatin kasar ta sanar da tsarinta na tayar da komadar tattalin arzikinta, a wani mataki na kwantar wa da ‘yan Najeriya hankali.
Mr. Emefile ya ce, kasar za ta fice daga wannan matsalar ta koma-bayan tattalin arziki nan da watan Disamba mai zuwa, kuma daga nan ne tattalin arzikin zai kama hanyar habbaka.
Emefile ya kara da cewa,’yan kasuwa daga kasashen waje, sun zuba jarin Dalar Amurka biliyan 1 a cikin watanni biyu da rabi da suka wuce.
Sannan ya ce, a cikin wannan makon, za a sake zuba jarin Naira biliyan 374 don kara karfafa tattalin arzikin da ke cikin wani hali
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da jama’a ke ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwa da karancin kudi saboda halin da kasar ta tsindima.