Valencia ta dauki tsohon dan kwallon Manchester United, Nani daga kulob din Fernerbahce, amma ba a bayyana kudin da aka sayo shi ba.
Nani wanda ke buga wa Portugal gasar cin kofin Turai, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku a Valencia.
Dan kwallon wanda ya fara murza-leda a Sporting Lisborn, ya koma Fernabahce da taka leda daga Manchester United a shekarar 2015.
Nani wanda ya lashe kofunan Premier da na zakarun Turai a Old Trafford, ya buga wa Fernabahce wasanni 46 ya kuma ci mata kwallaye 12, bayan da kungiyar ta yi ta biyu a gasar Turkiya da aka kammala.