
Asalin hoton, Getty Images
Kwallon da Ansu Fati ya ci a minti na 103 itace ta bai wa Barcelona nasara
Cikin wani yanayi na dakyar na sha, Barcelona ta tsallake rijiya da baya a wasan Copa del Rey da ta fafata da Intercity.
Ansu Fati ne ya jefa kwallo ta hudu a karin lokacin da aka yi, wanda hakan ya ba su nasara kan Intercity da ke buga matsayi na uku na gasar Sifaniya.
Oriol Soldevila wanda ya bar Birmingham City a bara ne ya jefa wa kungiyar ta La Liga kwallo uku rigis a raga.
Ya fara farke wadda Ronald Araujo ya fara ci a wasan kafin ya kara zare wadda Ousmane Dembele ya ci.
A minti na 77 ne Rapinha ya kara cin kwallo ta uku ga Barcelona ita ma Soldevila ya kara farke ta.
Hakan dai yakai kungiyoyin biyu ga karin lokaci, a nan ne kuma Fati ya jefa kwallon da ta bai wa Barcelona damar tsallaka wa zagayen ‘yan 16.