Nasarar da Secondus ya samu ta kara jefa jam’iyar PDP cikin sabon rikici


Uche Secondus tsohon shugaban riko na jam’iyar PDP shine ya kasance mutumin da ya lashe zaɓen kujerar shugabancin jam’iyyar adawa ta PDP.

Secondus wanda ya kada abokin hamayyarsa Tunde Adeniran da kuma Raymond Dokpesi.

Da kuri’a 66 Dokpesi ya kasance na uku a zaben yayin da Adeniran ya zo na biyu da kuri’a 230, Secondus ya lashe zaben da kuri’a 200.

Nasarar da ya samu ta jawo martani marar daɗi daga mutane da wasu  ya’yan jam’iyyar biyo bayan bayyana da sunansa yayi jikin jerin wasu sunaye da aka ce anyi amfani da su wajen murda zaɓen.

Dokpesi yace jerin sunan yan takarar  da wasu gwamnoni suka samar an raba shi ga wakilai masu kada kuri’a gabanin a fara gudanar da zaɓe.

Yace  sunayen mutane 21 dake cikin jerin sunayen da gwamnonin suka samar shine ya kasance suna na farko a cikin jerin sunayen ko wane wurin kada kuri’a.

A nasa ɓangaren Adeniran ya fice daga wurin taron lokacin da ake tsaka da kirgen kuri’a.

Kana daga bisani yayi  kira da asoke zaben gaba daya.

Ba wai Dokpesi da Adeniran kaɗai bane basu gamsu da zaben ba wasu mutane da yawa ma sun yi korafi inda daya daga cikin wakilai masu kada kuri’a yayi kira da a fara shirin binne jam’iyyar domin ta riga ta mutu a siyasance.

“Kawai sai mu siyo akwatin gawa mu binne jam’iyyar,” ya fadi cikin fushi.

Masu lura da al’amuran yau da kullum naganin cewa zaben shugaban da jam’iyar ta gudanar na ranar Asabar zai kara jefa ta cikin tsaka  mai wuya duba da yadda wasu mutane suka kakabawa ya’yan jam’iyyar yan takara.

A taron da aka gudanar na jiga-jigan jami’iyar da suka fito daga yankin arewa maso yamma sai da aka tashi baran-baran har ta kai ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa Namadi Sambo ya fice daga wurin taron cikin fushi.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like