Nasarar Trump Da Yadda Zai Shafi Amurka Da Abokan Huldarta. 


Maganar gaskiya shine samun nasarar Donald Trump ba abu ne da yake da mamaki ba saboda tun kafin zaben alamun sun gwada cewa shi zai lashe zaben. Duk da haka jama’a sun kauce wa zahiri sun aminta wa ransu cewa Trump ba zai samu nasara ba, shi kuma sai ya samu nasarar ta wannan dama.

Donald Trump mutum ne da za’a siffanta shi da kausasa kalamai da kuma tinkarar lamura da karfin tsiya. Za mu iya fahimtar wannan idan muka dubi kalaman shi yayin yakin neman zabe inda ya bawa duniya mamaki da ya ce matsalar kasar Amurka shine bakin haure musamman ma Musulamai. Wannan kadan ne daga cikin maganganu da Trump ya yi wadanda hatsarin su ya yi matukar tasiri wajen cin zaben shi.
Amurka kasa ce wacce shugaba daya baya iya juya ta kurum yanda yaso. Kasa ce da take kan kangararrun tsari da basa iya canzuwa saboda karfin da aka sanya musu. Wadannan tsari kuwa suna nan har yanzu. Ko Trum ko durum, babu wanda zai iya sauya su. Haka nan kuma kowani shugaba zai cigaba da bin wannan tsari ba tare da ketare ko kwayan zarra ba.
Wadannan tsari da kasar ke kai wadanda suka hada da fiskan tsaro, tattalin arziki da kuma hulda da kasashen duniya –  an tsara su ne musamman saboda tabbatar da manufar kasar na zama alakakai a idon duniya ta hanyan barazana ga kasashe. Idan muka dubi abunda ya faru a Iraqi, Libiya, Syria, Afganistan da sauransu, za mu fahimci cewa kasar Amurka shugaba ba ya canza manufarta. Wannan ya sa shugaba Obama ya kasa aiwatar da da yawa daga cikin tsarin da ya taho da shi ciki har da shirin shi na shafe shahararren fursunan nan na Gwantaramo. Fursuna ne da ake kai mutane ba tare da hukuncin alkali ba kuma babu ranan fitowan su.
To amma abun tambaya anan shine yaya duniya zata ji da Donald Trump a matsayin shugaban kasan Amurka?
Duk da tsarin da suka taho dasu, yawancin shuwagabannin Amurka sun fiskanci kalubale da basu yi tsammani ba. Bill Clinton ya fama da yaki a Yugoslavia. George Bush ya fama da harin 9/11. Barrack Obama ya fama da yakin basasa na Syria dakuma fada na Ukraine.
Duk da haka, wadannan shuwagabanni kowa da yanda ya bi da kalubalen gwamnatin shi. Amma Trump ga alama zai kasance barazana ga duniya yayin fiskantar duk wata kalubale da zata tinkari gwamnatin shi. Alamu sun tabbatar da cewa bashi da sauki wajen tinkarar lamura. Rashin saukin shi wajen tinkarar lamura kadai babban kalubale ne ga gwamnatin shi da duk wata kasa da take hulda da Amurka.
Kalubale na biyu ga kasar Amurka shine alakar kasuwanci tsakanin kasar Amurka da kasashe masu tasowa.  Kasancewar barazana da Donald Trump yayi a wurin yakin neman zaben shi, da yawa kasashe zasu juya wa kasar Chana wacce take kishiyan Amurka a idon duniya a kasuwanci. Wannan kuwa zai iya kasancewa dama mafi girma ga kasar Chana.

Idan muka dubi gefen ta’addaci da ‘yan ta’adda, Donald Trump a matsayin shugaban kasan Amurka zai kara dankara kasar cikin hatsarin kungiyoyin ‘yan ta’adda saboda kalam shi marasa kan gado. ‘Yan kasar Amurka da suke kasuwanci a kasashe da kuma kadarorin ‘yan kasar zai kasance cikin hatsari saboda kalaman batanci da da zababben shugaba yayi akan larabawa da musulmai.
Wadannan kalubale barazana ne ga kasar Amurka da abokan huldan ta. Babu shakka kalaman Trump sun jefa abokan huldan Amruka cikin rudani da tsoro saboda ikirarin shi na amfani da makaman nukiliya da kuma shirin shi na tsokanan tattalin arzikin Chana. Kasancewar kasar Amurka kasa da take shiga ko ba’a kasa da it aba cikin kasashe, hakan na nuna cewa wannan karo sabon shugaban ta yana da karancin hangen nesa da zai bawa kasar daman hulda da kasashe.
Trump ya yi alkawarin cewa zai dakile yarjejeniyar nukiliya tsakanin kasar da kasar Iran. Wannan zai dada sanya kasar Amurka cikin zargi daga kasashen duniya na neman tada tarzoma. Kowa yasan ruwa da tsaki da Amurka ke takawa wajen ganin cewa ta hana kasashe mallakan nukiliya. Wannan yasa duk kasan da tayi ikirarin nukiliya sai kasar Amurka tayi ca a kanta.
Trump ya riga ya fadi warwas a idon bakin haure da Musulami mazauna kasan Amurka wadanda ke dauke da sama da kaso 65 na yawan al’umman kasar. Wannan ya sa tun bayan cin zaben Trump ake samun zanga zanga a kasar wanda yanzu haka yana kara ta’azzara.
Kasashen musulmai babu shakka zasuyi nesa da kasar Amurka har zuwa lokacin da Trump zai sauka. Wannan zai faru ne saboda nuna tsagwaron kyama da Trump din yake yi ga Musulmai. Wannan kuma zai kasance ya shafi kasar Amurka sosai a bangaren tattalin arziki.

You may also like