Wani matashi mai shekaru 28 da haihuwa Nwaka John, da ke cikin tawagar ‘yan Nijeriya da aka ceto daga kangin bauta a kasar Libya, sun isa jihar Legas da yammacin Alhamis din da ta gabata, kuma ya baiyana wa manema labarai irin ukubar da suka fuskanta a kasar.
Mujallar Daily Post, ta wallafa cewa matashin dake daya daga cikin mutane 157 ‘yan Nijeriyar da aka maido gida daga kasar Libya, ya bayyana cewa sai da ya kai ga shan fitsarin wani mutum don kawai ya rayu.
John, wanda dan asalin jihar Imo ne, wanda ke da digiri a fannin injiniya na na’ura mai kwakwalwa, ya bar Nijeriya ne ranar 23, ga watan Yuni, na shekarar 2017, da niyar shiga nahiyar Turai, amma ya tsinci kansa a wannan kasa dake arewacin Afirka.
Matashin ya ce “na kwashe kwanaki 5 a cikin hamada, daga karshe sai da na sha fitsarin wani mutum domin na rayu”
Ya kuma kara da cewa a cikin mutane 104 da suka kama hanya, 81 ne kadai suka kai kasar Libya, sauran mutane 23 duk sun rasu a hanya cikin hamada.