Nasir Idris Na Jam’iyyar APC Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar KebbiDan takarar jam’iyyar APC a jihar Kebbi Dakta Nasir Idris (Kauran Gwandu) ya lashe zaben gwamna da aka kammala ranar Asabar 15 ga watan Afirilu, 2023.

Jami’in tattara sakamakon zabe farfesa Yusuf Sa’idu na jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto ne ya gabatar da sakamakon zaben.

Dakta Nasir Idris

Dakta Nasir Idris

Yace Dakta Nasir Idris ya samu kuri’a 409,225 inda ya doke dan takarar jam’iyyar PDP Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya wanda ya zo na biyu da kuri’a 360,940. Hakan nan nufin kuri’u 48,285 ke tsakanin ‘yan takarar.

Wannan sakamakon dai ya nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta kara samun kujerun gwamna.Source link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like