Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya Aisha Buhari ta yi ikirarin cewa ta yi matukar bakin ciki a lokacin da ta samu labarin harin da jirgin yakin Nijieriya ya kai sansanin ‘yan gudun hijirar kauyen Rann bisa kuskure.
Haka kuma Uwargidan Shugaban kasar ta jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su inda ta yi masu fatan Ubangiji ya ba su juriya kan rashin da suka yi na wadanda suka rasa rayukansu tare kuma da yi wa sojojin Nijeriya addu’ar samun galaba kan mayakan Boko Haram.