Duk da cewa jarrabawar ta bana ba’a kammala turo sakamakon ta ba, amma mafi yawa an turo musu sai dai sakamakon babu dadin gani.
Mafiyawan dalibai da suka zana wannan jarabawar a wannan shekara, ba su samu sakamakon da suke bukata na zuwa jami’a ba.
Ba za’a iya kwatanta adadin daliban da suka fadi a dai-dai wannan lokaci ba, sai dai mafi yawa sun sha kasa.
Babu wani rahoto, ko cikakken bayani daga hukumar ta JAMB game da faduwar daliban.
Lallai idan aka ci gaba da tafiya haka, to babu shakka ci baya ba zai kare a Nijeriya ba.
Kasancewar mafi yawan daliban da suka zana jarrabawar ‘ya’yan talakawa ne, wadanda iyayensu ba su zarafin daukar nauyin karatunsu zuwa kasashen waje, domin huce musu takaicin hukumar.
A wannan shekara da kuma shekarar da ta gaba an rubuta jarrabawar ne, da na’ura mai kwakwalwa (Computer). Kuma ga shi mafiyawan daliban da suka zana jarrabawar a gidajensu ba’a amfani da na’urar, dan haka za mu fassara wannan faduwa ta wannan dalili, ba wai takkwalci ne ya sa suka fadi ba!
Muna kira da babbar murya ga hukumar cewa; ya kamata ta gaggauta gyara sakamakon ta fitar na wannan shekara, domin ba zai kawo wa kasarmu ci gaba da kuma hanya mai bullewa ba.
Duk kasashen duniya suna alfahari da ilimin da ‘yan kasa suke da shi, amma a Nijeriya yunkurin neman gurbin karatu na neman ya gagari ‘yan kasa.