NDLEA Ta Cafke Masu Safaran Miyagun Kwayoyi Da Hodar Iblis a LegasIta dai wannan hoda ta iblis an kiyasta kudinsa ya kai na $278,250 kwatankwacin Naira biliyan 194,775.

Wadanda aka kaman sun hada da wani dan kasar Jamaica da kuma wasu yan Najeriya 7, wadanda aka kama a sassa daban daban na birnin lagos.

Da yake zantawa da ‘yan jarida, kakakin hukumar Mr Demi Babafemi, yace sun samu hadin kai daga hukumomin yaki da safaran miyagun kwayoyi na kasa da kasa musanman na kasar Amurka.

Yace “wadannan mutane da kuke gani mun kama su ne domin bincike ko zargi da muke masu da hada hadar muggan kwayoyi na hodar iblis. Wannan gida da kuke gani gidane da a waje zaku zaci babu kowa a ciki, amma gida ne da ake anfani dashi wajen ajiye muggan kwayoyi, kuma suna aikin su ne da hadakar kungiyoyin safarar muggan kwayoyi na duniya. Kuma tun a shekara ta 2018 muke binciken su, kafin mu diran masu.”

Tuni dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke ziyara a kasar Amurka ya godewa shugaban hukimar ta NDLEA bisa wannan namijin kokari na kama yan safaran muggan kwayoyi da hajojin su.

You may also like