NDLEA ta gano ganyen tabar wiwi da kuɗinta ya kai miliyan ₦20



Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi Ta Ƙasa NDLEA ta gano wani abu da ake tunanin ganyen tabar wiwi a wani dakin ajiye kayayyaki dake Dajin Ugbubezi  a ƙaramar Hukumar Owan ta Yamma dake jihar Edo.

Kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar Edo, Buba Wakawa ya bayyana haka cikin wannan wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba a Benin.

Wakawa ya ce jami’an sun gano ganyen da ake zargi na tabar ta wiwin ne mai yawan gaske wacce ba a dade da girbinta ba  a wani dakin ajiye kayayyaki dake Dajin Ugbubezi.

Yace darajar ganyen tabar wiwin a kasuwa ya fi naira miliyan 20 jami’an hukumar ne sama da 70 suka ɗauke ta daga dakin ajiye kayayyakin.

Mutane biyu da ake zargin mambobi ne na gungun masu safarar miyagun kwayoyi aka kama kuma ana cigaba da yi musu tambayoyi.

Kwamandan na NDLEA ya ce an gano wurin ne bayan da hukumar ta samu wasu bayanan sirri.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like