
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ta ce ana fakewa da noman kayan lambu a gonakin na wiwi
Hukumar da ke yaki da miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce ta gano gonaki uku da ake shuka ganyen wiwi a jihar Katsina.
Mataimakin shugaban hukumar mai kula da harkokin gudanarwa a jihar, Halilu Hamidu ya ce sun samu nasarar gano gonakin ne bayan samun bayanai daga wasu mutane.
Hamidu ya ce wannan shi ne karon farko da hukumar ta gano irin wannan gonar a kauyen Sobashi na karamar hukumar Dutsi.
“Masu gonar suna amfani da ita wajen shuka tabar ta wiwi amma suna fakewa da noman kayan lambu irinsu tattasai da tumatur,” in ji shi.
jami’in na NDLEA ya kara da cewa hukumar ta kama mutum daya sannan tana bibiyar sawun sauran abokan huldarsa.
Ya kara da cewa: “Akwai mutum daya da muka cafke sannan muna da yakinin kama sauran manoma tabar domin kuwa muna samun bayanai sannu ahankali”
A cewar hukumar ta NDLEA wannan shi ne karon farko da ta gano gonakin shuka wiwi masu yawa irin wadannan a jihar ta Katsina.
Mataimakin shugaban hukumar mai kula da harkokin gudanarwa a jihar ya kara da cewa a daya bangaren hukumar ta kama sinadarin Kodin da darajarsa ta kai Naira miliyan goma.
NDLEA ta kara da cewa ba karamin hadari wadannan miyagun kwayoyin suke da su ga al’umma ba.
Katsina na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke iyaka da Jamhuriyar Nijar, inda masu fasakwaurin haramtattun kayayyaki ke iya safararsu a tsakanin kasashen biyu.