NDLEA ta kama mutane 2 kan laifin mallakar makamai, 77 kuma da laifin safarar miyagun kwayoyi


Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA, a jihar Bayelsa ta kama wasu matasa biyu da laifin mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba da kuma wasu mutane 77 kan safarar miyagun kwayoyi.

Hukumar tace an samu bindiga ɗaya kirar AK-47 da kuma wata bindigar guda ɗaya daga hannun mutanen yayin da aka kama su.

Da yakewa yan jaridu jawabi a Yenagoa, kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar, Abdullahi Abdul yace an kama mutaneb da ake zargi ne a ranar Talata lokacin da jami’an hukumar suke gudanar da sintiri.

A cewar Abdul an kama mutanen da ake zargin ne a ranar 1 ga watan Disamba lokacin da suke fasa kwaurin makaman daga Ughelli a jihar Delta zuwa jihar Rivers akan kuɗi ₦50000 daga wani mutum wanda ake nema ruwa a jallo.

Ya kuma ce ragowar mutane 77 da aka kama da laifin safarar miyagun kwayoyi an kama sune tsakanin watan Oktoba da Nuwamba cikinsu akwai maza 54 da kuma mata 23.

Miyagun ƙwayoyi dake da nauyin kilogiram 124.342 aka samu daga hannun waɗanda ake zargi da aikata laifin.

You may also like