Neman shugabancin Tarayyar Afirka


 

 

Kasashe uku na Afirka za su fito da ‘yan takara domin neman shugabancin Tarayyar Afirka.

Kasashen Kenya, da Chadi, da kuma Senegal za sui fito da ‘yan takara wadanda za su fafata neman shugabancin hukumar Tarayyar Afirka domin maye gurbin Nkosazana Dlamini-Zuma. Sunayen sun hada da ‘yan takara Amina Mohamed ministan harkokin wajen Kenya, da Moussa Faki Mahamat daga Chadi, da kuma dan Senegal Abdoulaye Bathily wanda yake zama jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Akwai kuma ‘yan takara biyu daga kasashen  Equatorial Guinea da Boswana wadanda wadanda suka gaza samun abin da ake nema lokacin da aka kada kuri’ar farko a watan Yuli da ya gabata. Ita dai shugabar hukumar Tarayyar Afirka Dlamini-Zuma ta fitar da kanta daga sake neman matsayin na karin wasu shekaru hudu, kuma ana sa ran taron shugababnin kasashen Afirka na watan Janairu a birnin Addis Ababa fadar gwamnatin Habasha zai zabi sabon shugaban hukumar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like