An nemi MDD ta shiga tsakanin Pakistan da Indiya


 

Gwamnatin Pakistan ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakanin sabon rikici da Indiya.

Indien Sicherheitskräfte an der Grenze mit Pakistan (Getty Images/AFP/N. Nanu)

Gwamnatin Pakistan ta nema Majalisar Dinkin Duniya ta taimaka wajen dakile zamantankiya taksanin kasar da Indiya kan yankin da ake takaddama na Kashmir.Jakadan kasar ta Pakista da ke majalisar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP abin da ke faruwa a yankin yana da hadari, sannan ya kara da cewa muddun kasashen duniya suka zuba ido lamarin takasanin Pakistan da Indiya zai kasance. Mai magana da yawun majalisar ya ce suna shirya da shiga tsakani domin kawo karshen zaman zullumi.

A wani labarin Majalisar Dinkin Duniya ta ce dakarunta masu saka ido suna bincike kan zargin karya yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Kashmir bisa iyaka tsakanin Pakistan da Indiya.

You may also like