
Asalin hoton, Getty Images
Jam’iyyun masu ra’ayin riƙau sun samu ƙarin goyon baya a zaɓen watan Nuwamba
Wata sabuwar gwamnati da aka amincewa da kafawa, kuma ake gani ita ce mafi cike da masu ra’ayin riƙau a tarihin Isra’ila, ta cika sharaɗin sake komawar Benjamin Netanyahu kan karagar mulki.
Mr Netanyahu, wanda ya lashe zaɓe a watan Nuwamba, na shirin fara wa’adin mulki mai cike da tarihi a matsayin fira minista karo na shida.
Gamayyar gwamnatinsa ta ƙunshi jam’iyyu ‘yan ra’ayin riƙau ciki har da wani jagoran jam’iyya da kotu ta taɓa hukuntawa a kan laifin ƙin jinin Larabawa.
Falasɗinawa na fargaba sabuwar gwamnatin za kuma ta ƙarfafa ikon Isra’ila a yankin Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye.
“Na yi ƙoƙari [na kafa gwamnati],” Mista Netanyahu ya wallafa a shafin Tuwita, mintuna ƙalilan kafin sha biyun dare agogo Isra’ila kamar yadda Shugaba Isaac Herzog ya gindaya.
Abokan ƙawancen Mista Netanyahu sun yi watsi da aƙidar kafa ƙasa biyu don kawo ƙarshen rikicin Isra’ila da Falasɗinawa – bisa tsarin zaman lafiya da ƙasashen duniya ke mara wa baya, da burin ganin ƙasar Falasɗinu mai ‘yancin cin gashin kanta a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ke maƙwabtaka da Isra’ila, inda birnin Ƙudus zai kasance babban birnin tarayya na ƙasashen biyu.
Jagoran jam’iyyar tabbatar da aƙidar Yahudanci ta Religious Zionism, mai ƙawance da sauran jam’iyyu masu tsananin ra’ayin riƙau biyu, da ke matsayi na uku a yawan kujeru a majalisar dokokin ƙasar knesset, na da burin ganin Isra’ila ta haɗe Gaɓar Yamma da Kogin Jordan kuma a ba ta faffaɗan iko kan harkokin da za ta gudanar a can.
Isra’ila ta mamaye Yamma da Kogin Jordan da Gabashin Ƙudus da Zirin Gaza ne a yaƙin 1967.
Yahudawa ‘yan kama wuri zauna fiye da 600,000 ne ke rayuwa a Gabashinn Ƙudus da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
A ƙarƙashin dokokin duniya ana ɗaukar waɗannan matsugunnai matsayin haramtattu, ko da yake Isra’ila ta musanta hakan.
Isra’ila ta janye dakaru da ‘yan kama wuri zaunanta daga yankin Zirin Gaza a shekara ta 2005.
‘Yan adawa a Isra’ila da kuma atoni janar ɗin ƙasar, sun yi gargaɗin cewa garambawul ɗin da sabuwar gwamnati mai jiran gado ke shirin yi – ciki har da bai wa ‘yan majalisar dokoki damar rushe hukunce-hukuncen Kotun Ƙoli – wata barazana ce da za ta yi zagon ƙasa ga tsarin dimokraɗiyyar Isra’ila.
Abokan ƙawancen sun kuma ƙuduri aniyar kawo gyaran fuska na doka wanda zai kawo ƙarshen shari’ar da Netanyahu ke ci gaba da fuskanta a kan tuhume-tuhumen cin hanci da almundahana da kuma cin amana.
Netanyahu dai ya sha cewa shi bai aikata wani ba daidai ba.
‘Yan adawa da ƙungiyoyin kare haƙƙin fararen hula na Isra’ila sun bayyana fargaba musamman a kan shigar da masu tsananin ra’ayin gurguzu cikin sabuwar gwamnati.
Shugaban jam’iyyar Otzma Yehudit (Ikon Yahudawa) Itamar Ben-Gvir ya yi suna wajen furta kalaman ƙin jinin Larabawa kuma yana kira a sassauta dokoki a kan lokacin da dakarun tsaro za su iya buɗe wuta idan sun fuskanci barazana.
Mutumin da aka taɓa samu da laifin nuna wariyar launin fata da goyon bayan wata ƙungiyar ta’addanci, shi ne ke shirin zama ministan tsaron ƙasa da ke da iko kan ‘yan sanda a Isra’ila da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Wani mai matsanancin ra’ayin riƙau a gwamnatin, Avi Maoz na jam’iyyar Noam ta masu ƙin jinin ‘yan luwaɗi da maɗigo, ya yi kira a haramta shagulgulan birnin Ƙudus na Masu Alfahari da harkar Luwaɗi, kuma bai yarda da bai wa mata dama iri ɗaya a rundunar sojin ƙasar ba, sannan yana so a iyakance shiga Isra’ila ga Yahudawa kawai don hakan ya dace da tsantsar fassarar dokar Yahudanci.
Benjamin Netanyahu ya zargi masu sukar lamirin da kasancewa masu baza labaran da ke kaɗa hantar cikin mutane kuma ya yi alƙawarin ci gaba da al’amura kamar yadda aka saba.
“Zan sa hannu biyu na riƙe harkoki ƙam-ƙam,” ya faɗa wa kafa yaɗa labaran Amurka NPR a makon jiya. “Ba zan bar wani ya taɓa ‘yan luwaɗi da maɗigo ba ko ya hana wa Larabawa ‘yan ƙasa ‘yancinsu ko wani abu makamancin haka, ba zai taɓa faruwa. Kuma lokaci ne zai yi alƙalanci.”