New York ta amince a rinƙa mayar da gawarwaki ɓurɓushin ƙasa..

Asalin hoton, Getty Images

Jihar New York ta zama jihar Amurka ta baya-bayan nan da za ta bayar da dama a rinƙa mayar da gawarwaki ƙasa.

Hakan na nufin mutum zai iya bayar da umarni a mayar da gawarsa ƙasa idan ya rasu – wanda wasu ke ganin hakan yana da kyau ga muhalli maimakon a binne mutum ko kuma a ƙona gawarsa.

Idan za a yi hakan, akan saka gawar mutum ne a cikin wani akwati a rufe shi tsawon makonni domin gawar ta ruɓe bayan an gauraya ta da wasu abubuwan da za su taimaka ta zama ƙasa.

A 2019, Washington ta zama jihar Amurka ta farko da ta halasta wannan lamari. Sai kuma daga baya Colarado da Oregin da Vermont da California suka biyo baya.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like