
Asalin hoton, Getty Images
James Maddison
Newcastle United za ta yi gogayya da Manchester City wajen sayen ɗan wasan Ingila na tsakiya James Maddison, 26, daga Leicester City. (Northern Echo)
Manchester United na zawarcin ko dai ɗan wasan Tottenham kuma kyaptin din Ingila, Harry Kane, 29, kan £100m ko kuma ɗan wasan Najeriya mai buga wa Napoli, Victor Osimhen, 24 inda kocin Man U ɗin Erik ten Hag ke neman ɗan wasan gaba na duniya. (Telegraph)
Nan bada daɗewa ba masu zuba jari na Qatar za su yi tayin sayen Manchester United da suke da yaƙinin za ta lashe duk wata gasa inda iyalin Glazer da suka mallaki ƙungiyar ke neman sayar da ita kan £6bn. (Mail)
Manchester City na kwaɗayin doke Real Madrid da Liverpool wajen sayen ɗan wasan Ingila mai shekara 19 Jude Bellingham daga Borussia Dortmund a bazara – amma fargabar takunkumi bayan tuhumar da aka yi musu a Premier League na iya hana su yin haka. (Telegraph)
Borussia Dortmund na shirin janyo hankalin Bellingham ya ci gaba da zama a Jamus zuwa wata kakar wasa. (90min)
Watakila Arsenal ta yanke hukunci kan cefanar da ɗan wasa Folarin Balogun a bazara duk da ƙwallaye 14 da ya zura cikin wasa 21 da ya buga wa Reims a gasar Ligue 1. (Sun)
Bayanai na cewa Kocin Rayo Vallecano Andoni Iraola na cikin manyan waɗanda ke neman maye gurbin Jesse Marsch a matsayin kocin Leeds United. (Independent)
Liverpool da Manchester United sun soma tattaunawa kan yarjejeniyar ɗan wasan Eintracht Frankfurt Randal Kolo Muani, mai shekara 24. (L’Equipe, via Metro)
Tattaunawar Manchester United kan ƙulla sabon kwantiragi da ɗan wasan Portugal, Diogo Dalot na ci gaba da kankama, ma’ana zai yi wahala ga Barcelona ta sayi ɗan wasan mai shekara 23. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Mai bugawa Faransa tsakiya Adrien Rabiot, 27, da ya kusa shiga Manchester United bara, na daga cikin ƴan wasa biyar na farko da Juventus za ta cefanar. (Gazzetta dello Sport, via Mirror)
Inter Milan ta tattaunawa da ɗan wasan gaba na Argentina Lionel Messi, 35, kafin tsohon mai bugawa Barcelonan ya yanke shawarar zuwa Paris St-Germain. (Goal)
Mai buga wa Roma kuma ɗan Italiya, Nicolo Zaniolo, 23, ya yi bulaguro zuwa Instanbul domin kammala tattaunawa kan komawarsa Galatasaray. (Mail)
Ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya ta yi wa ɗan wasan tsakiya na Spaniya Sergio Busquets, 34, tayin yerjejeniyar shekara biyu kan kuɗi £16m kowace kaka amma za ta jira ta ga ko Barcelona za ta sabunta kwantiraginsa kafin yanke shawarar. (Mundo Deportivo – in Spanish)