Newcastle United na zawarcin Neymar, idanun Chelsea na kan Messi



.

Asalin hoton, Getty Images

Newcastle United na zawarcin dan wasan gaba na Brazil, mai taka leda a Paris St-Germain Neymar, mi shekara 31, a daidai lokacin da suke duba ‘yan wasan da za su saya a kaka mai zuwa.

Chelsea na sahun gaba a kungiyoyin da ke sin daukar dan wasan gaba na Lionel Messi, mai shekara 35, idan kwantiraginsa ya kare a PSG. (Football London)

Wolves sun yi wa Barcelona ta yin fam miliyan 30 kan dan wasan tsakiya na Portugal Ruben Neves, mai shekara 26, da kuma dan wasan tsakiya na Sifaniya Ansu Fati, dan shekara 20. (Relevo – in Spanish)

Barcelona ta karkata akalar zawarcin ta ga dan wasan tsakiya na Morocco Sofyan Amrabat, mai shekara 26, daga Fiorentina, wanda hakan ka iya karawa kungiyar Arsenal fatan dauko dan wasan tsakiya na Sifaniya Martin Zubimendi, 24, daga Real Sociedad. (AS – in Spanish)



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like