Neymar ya koma atisaye zai fuskaci Bayern Munich kenan



Neymar

Asalin hoton, Getty Images

Neymar ya koma atisaye a lokacin da Paris St Germain za ta buga wasa uku nan gaba masu mahimmaci.

Dan wasan tawagar Brazil, bai yi wa PSG karawa biyu ba – wasan Ligue 1 da ta doke Montpellier da kuma Toulouse – sakamakon jinya da ya yi.

Kenan dan kwallon yana da damar buga wa PSG wasan hamayya da za ta yi da Marseille ranar Laraba a karawar ‘yan 16 a Coupe de France.

Haka kuma PSG wadda ke jan ragamar teburin Ligue 1 za ta kece raini da Monaco ta hudu a babbar gasar tamaula ta Faransa ranar Asabar.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like