Tsohon Gwamnan Neja, Babangida Aliyu ya musanta rahotannin da ke nuni da cewa yana shirin ficewa daga PDP ya koma jam’iyyar APC inda ya jaddada cewa ba zai taba barin jam’iyyar ba.
Ya ce, ” Duk da cewa jami’iyyar PDP na fama da wasu ‘yan matsaloli da yanzu haka muna kokarin ganin mun warware su, hakan ba zai sa in canza sheka ba, ina na tare da PDP don ko ita ce ta yi sanadiyyar zama na gwamna a 2015.