Ni Da Ojukwu A Shekarar 2003 Mun Amince Najeriya Ta Cigaba Da Zama Kasa Daya -Buhari  


Shugaban kasa Muhammad Buhari yace shi da marigayi  Chukuemeka Ojukwu, shugaban al’ummar Igbo sun amince cewa Najeriya taci gaba da zama kasa daya.

Ojukwu ya jagorancin fafutukar kafa kasar Biyafara a shekarar 1967 zuwa 1970.Yanzu dai wasu kungiyoyi a yankin kudu maso gabas na fafutukar farfado da kafa kasar ta Biyafara.

A cikin jawabin da yayiwa yan kasa a safiyar yau Litinin, Buhari yace shi da Ojukwu sun zauna sun duba matsalolin kasarnan  lokacin da marigayi jagoran kabilar ta Igbo yakai masa ziyara a Daura cikin shekarar 2003 inda a karshe suka amince da kasarnan dole ta cigaba da zama kasa daya.

Shugaban kasar ya kuma bayyana rashin jin dadinsa kan yadda kalaman nuna kiyayya ke cigaba da yaduwa a kafafen sadarwa na zamani.
” A shekarar 2003 bayan da na shiga siyasa,marigayi Emeka Ojukwu yazo gidana dake garinmu Daura a matsayin bako.Cikin kwanaki biyu munyi tattaunawa mai tsawo har takai mu cikin dare domin gano matsalar Najeriya.Dukkanmu mun amince da cewa kasarnan ta cigaba da zama kasa daya mai hadin kai. ”

Buhari ya kuma bayyana cewa duk dan Najeriya yana da damar zama a duk inda yake so cikin Najeriya.

You may also like