Ni Musulmi ne Amma Inason Zuwa Coci -Idris Okuneye Bobrisky


Fitaccen mai shigar Matan nan mai suna Idris Okuneye wanda aka fi Sani da Bobrisky ya yi ikirarin cewa shi Musulmi ne amma tun yana dalibi a jami’a yake son bin abokansa zuwa yin ibadarsu a coci.

Okuneye wanda dan asalin jihar Ogun ne ya nuna cewa iyayensa duk Musulmi ne amma saboda yanayi sana’arsa na kasancewa cikin kwalliya a kowane lokaci ya tilasta daina yin Sallah saboda idan har zai yi alwala to, sai ya sake yin wani sabon kwalliya.
Ya ce ya yanke shawarar daukar dabi’ar shigar mata ne saboda ya yi fice inda ya tabbatar da cewa duk da yake yana da masoya amma kuma akwai wadanda suke nuna kyama gare shi.

You may also like