Ni Nake Daukat Dawainiyar Kaina Idan Nayi Tafiya –  Aisha BuhariUwargidan Shugaban Kasa, Hajiya Aisha Buhari ta jaddada cewa a duk lokacin da ziyarci wata kasar waje, ita ce ke daukar nauyin akasarin abincin da take bukata ba ya ga dan tallafin da take samu daga Fadar Shugaban kasa idan har bukatar hakan ya taso.
Aisha ta yi wannan ikirarin bayan wani rahoton da kafar sanarwar ‘ Sahara Reporter’ ta wallafa a shafinta inda ta nuna cewa a duk lokacin da Uwargidan Shugaban ta ziyarci wata kasar waje, tana takurawa ofisoshin jakadanci wajen tanadar mata kayayyakin abinci na Alfarma.
Ta kuma musanta rahoton daukar tawaga mai yawa a yayin tafiyar inda ta nuna cewa tafiyar da ta san ta debi mutane da dama shi ne wanda ta yi ita da ‘ya’yanta uku, da mai tsaron lafiyarta sai kuma likatanta.

You may also like