Ni Zan Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2019 – FayoseGwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose yace ko shakka babu shine zai lashe zaben shugabancin kasar nan a zabukan shekarar dubu da goma sha Tara dake tafe.

Fayose ya bayyana haka a wani zama na musamma da yayi da mukarraban gwamnatin shi a fadar gwamnatin Jihar a Jiya Juma’a. 

Fayose yace tsofaffin gwamnonin Jihar Ekiti  Segue Oni, Kayode Fayemi da suke son kuma tsayawa takara a zabukan 2018 ai wahala suke baiwa kan su, ni kadai ne zan taba cin zango biyu a Jihar Ekiti nima irin ayyukan dana yi ne suka bani wannan damar.

You may also like