Tsagerun Niger delta da ke Najeriya sun sake fasa bututun mai na kamfaninin Delta Grrenland Mandate kamar yadda suka bayyana shafinsu na Twitter.
Kungiyar ta dauki alhakin kai hari kan bututun man na kamfanin da aka tarwatsa a ranar Larabar nan inda ta kuma ce, ta kai harin ne karkashin aiyukan da ta le na farfasa bututan kai da ke yankin.
Harin ya kuma shafi wani bangare na butun man karamain kamfanin samar da mai na Najeriya da ke yankin na Niger Delta.
Harin ya zo awanni 48 bayan da kungiyar ta yi barazanar kai hari kan bututan man na Najeriya.
Kungiyar dai ta aike da sakon gargadi ga shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa inda ta ce, za ta lalata matatun man fetur da suke kasar gaba daya.