Niger delta – Munyi shirin Fito Na Fito inji sojojin Najeriya 


Rundunar sojan Nigeria ta fara wani atisaye ka’in-da-na’in a yankin Niger Delta da aka yi wa take da”murmushin kada.”Atisayen dai wani mataki ne na kara horar da dakarun kasar da ke yankin, da kuma yunkurin murkushe ayyukan tada kayar-baya da hare-hare kan bututan mai da ake fuskanta a yankin na Niger Delta mai arzikin man fetur.
Atisayen ya hada da fito da manyan makaman yaki ana yawo da su a kan tituna, da dazuka da kuma ruwan da ke yankin.

Birgadiya Janar Hamisu Hasan kwamandan birgadiya ta biyu ta rundunar sojan Nigeria da ke jihar Rivers, ya shaida wa ‘yan jaridu cewa atisayen zai kara horar da sojoji sanin makamar aikin, da kuma aikewa da sakon gargadi ga duk wanda ke yi wa gwamnati zagon-kasa.

Ya ce a gwajin atisayen da suka yi a makon jiya, rundunar ta fatattaki wasu ‘yan ta’adda, ta kuma kashe wasu daga cikinsu, sannan kuma an samu makamai masu yawa.Ana dai zargin sojojin Nigeria da yin amfani da karfi fiye da kima, da take hakkin bil adama a duk lokacin da suke irin wannan aikin.To sai dai Janar Hamisu Hasan ya ce sojojin Nigeria na aiki bisa kwarewa, da sanin ya kamata.

You may also like