Nigeria- Masana sunce Dole ce tasa Najeriya cin Bashi


 

Masana tattalin arziki a Najeriya sun ce dole ce ta sanya Najeriya ciyo bashi daga ketare.A ranar Alhamis ne dai gwamnatin Nigeria ta ce za ta ciyo bashi daga cibiyoyin kasashen waje da suka hada bankin duniya da bankin raya kasashen Afirka da kuma Bankin Bunkasa kasashe na China.
Masanan sun ce babban dalilin da ya sa cin bashin shi ne irin wagegen gibin da kasar ta samu a kasafin kudin shekarar 2016.

Gwamnatin Muhammadu Buhari dai ta yi kasafin kudin 2016 irin wanda ba a taba yi ba a baya wanda ya kai Naira tiriliyan shida.To sai dai kuma daman akwai gibin Naira tiriliyan biyu, al’amarin da ya sa ake ta maganar samo rancen kudi domin cikashe gibin.

Sakamakon faduwar farashin mai a kasuwar duniya da tabarbarewar tattalin arzikin kasar, ya kara sanya kudaden shiga da Najeriyar ke samu sun yi kasa.

A ta bakin masanan, wannan ne dalilin da ya sa ya zama wajibi ga Najeriya ta ciyo bashi domin rufe gibin da ta samu.

Faduwar farashin mai dai ta jefa Najeriya cikin mawuyacin hali ta fuskar tattalin arziki.Ko da watan da ya gabata wasu alkaluma da aka fitar a kasar suka nuna cewa, kasar ta auka cikin karayar arziki.

Najeriya dai ta dogara ne akan albarkatun mai wajen samun kashi saba’in na kudin shigar ta.

You may also like