NIGERIA TA AMINCE DA KASAFIN KUDIN SHEKARA UKU. 


A Nigeria, gwamanti ta amince da tsarin kasafin kudi na shekara uku, inda ta yi hasashen samun bunkasar tattalin arziki na kashi 4 cikin dari.
Najeriya na kuma fatan hakan zai daidaita faduwar da kudin kasar, wato Naira ya yi a kasuwar musayar kudi.Gwamnati ta yi kiyasin farashin gaggan danyen mai zai zama $42 zuwa $50 a tsawon wannan lokaci.Za a tura tsarin kasafin kudin na matsakaicin zango zuwa majalisar dokokin kasar, domin ‘yan majalisar sunamince da shi.

You may also like