Nigeria Za Ta Tura Sojoji 800 Zuwa Darfur Don Aikin Tabbatar Da Zaman Lafiya


Babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Nijeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ya sanar da cewa Nijeriya za ta tura da sojoji 800 zuwa yankin Darfur na kasar Sudan don ci gaba da aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya.

Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Nijeriyan ya bayyana haka ne wajen biki yaye wasu sojoji 755 da suka halarci wata holarwa ta soji da aka gudanar da a barikin soji da ke Jaji, jihar Kadunan Nijeriya inda ya ce za a tura sojoji 800 zuwa yankin Darfur na kasar Sudan da nufin ci gaba da taimakawa shirin Majalisar Dinkin Duniya na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.

Janar Buratai wanda Kwamandan runduna ta daya ta sojin Nijeriyan dake Kaduna, Manjo Janar Adeniyi Oyebade ya wakilta ya ce Nijeriya din za ta ci gaba da tura kwararrun soji don gudanar da aikin  tabbatar da zaman lafiya a matsayin nata gudummawar wajen tabbatar da sulhu da zaman lafiya a duniya.

Ita dai wannan horarwar da aka ba wa sojojin da ake shirin tura su ayyukan tabbatar da zaman lafiya ne don su sami kwarewar da ake bukata a wannan bangaren.

You may also like