Nigeriya Zata Fara Fitar Da Shinkafa Waje A Karshen Shekarar 2017 -CBN


Babban Bankin Nijeriya ya yi hasashen cewa a karshen shekarar 2017, Nijeriya za ta fara fitar da shinkafa kasashen ketara.

A cikin wani rahoto, Bankin ya nuna cewa shinkafar da aka samu a bana ta wuce yawan wadda aka yi hasashen kuma a cewar Bankin inda hakan ya dore, Nijeriya za ta wadatu da shinkafar har ta samu rarar da za ta fitar don sayar wa a kasashen ketare.
Rahoton ya nuna cewa a fara shirin noman shinkafar ce a jihar Kebbi inda aka fara da manoma 78,000 a wani tsari ta yadda za su yi noman shinkafar sau uku a shekara wanda kuma a halin yanzu an samu fiye da tan milyan guda na shinkafa.
Rahoton ya ci gaba da cewa jihar Ebonyi ita ce ta biyu wadda ta rungumi shirin wanda kuma a halin yanzu an fara girbin shinkafar kuma ana sa ran samun fiye da tan milyan guda sai kuma jihohin Jigawa Sokoto da Cross Rivers.

You may also like