Nijar : An Cafke Mutane 38 Bayan Rikicin Manoma da Makiyaya


4bkb6a417216ebgty7_800c450

 

 

Rahotanni daga Jamhuriya Nijar na cewa ‘yan sanda sun cafke mutane 38 wadanda galibi matasa ne manoma, bayan rikicin da ya faru tsakanin manoma da makiyaya.

A kalla mutane 18 ne suka mutu yayin da wasu kimanin 40 suka jikkata a kazamin fadan daya barke Jiya Talata a kauyen Bangui dake jahar Tawa a yammacin kasar.

Bayanai sun nuna cewa rikicin ya faru ne a yayin da wasu dabbobin fulani suka shiga wasu gonaki manaman tare da lalata masu amfanin gona.

Tunda farko dai wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar wace ta kira lamarin da fada tsakanin manoma da makiyaya fulani ta tabbatar da mutuwar 18 ciki har da bakwai wadanda aka kona da ransu da suka hada da mata, yara da kuma tsofafi, baya ga gidaje 22 da aka kona.

Rikici tsakanin manoma da makiyaya fulani ba sabon abu ne a kasar ta Nijar, musamen a lokacin fitar da albarkacin gona da yake zuwa daidai lokacin da dabbobi ke tururuwa wajen filayen kiwo.

You may also like