Nijar ta yi wawan kamun kayan maye a kan iyakarta da Najeriya da BeninSmuggled drugs

Asalin hoton, Niger Gaya Prefet

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun bayyana damuwa kan ƙaruwar fasa-ƙwaurin miyagun ƙwayoyi a tsakanin iyakar ƙasar da Najeriya da kuma Jamhuriyar Benin.

Hakan na zuwa ne bayan da aka kama ɗaruruwan ɗauri na tabar wiwi da wata ƙwaya nau’in baliyam mai hatsari, da aka yi yunƙurin shigarwa ƙasar a ranar Juma’a daga wata ƙasa mai maƙwabtaka.

Shugaban gundumar Gaya a cikin jihar Dosso, kudu maso yammacin Nijar, Ashimu Abarshi ne ya yi wa BBC ƙarin bayani game da kama miyagun ƙwayoyi na baya-bayan nan.

Ya ce ƙwayoyin da suka kama sun haɗar da tabar wiwi ɗauri 400 da kuma ɗauri 1,260 na wata ƙwaya mai suna Diezepam, da kuma ƙarin ɗauri biyar na ganyen wiwi, da aka yiwo fasa-ƙwaurinsu a cikin kwale-kwale ta Kogin Isa.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like