NijerDelta: Dattawan Neja Delta Sun Nuna Rashin Gamsuwa da Shirin FarFado Da Yankin


A yayin da aka tsara tattaunawa tsakanin Shugaba Buhari da dattawan yankin Neja Delta a gobe Laraba, rahotanni daga yankin sun nuna cewa Dattawan sun nuna rashin gamsuwa da da shirin gwamnati na zuba Naira Tiriliyan hudu don farfado da yankin.
Rahotanni sun nuna cewa dattawan sun nuna cewa gwamnati ba ta da wadannan kudade da ta yi ikirarin narkawa a yankin inda suka nuna cewa tun da farko an tsara shirin ne ta yadda kamfanoni masu zaman kansu za su dauki nauyi amma kuma daga aka shigo da gwamnati ciki.

You may also like