A kwanan baya ne dai kungiyar ‘yan Niger delta suka amince da zasuyi sulhu da gwamnatin Najeriya. Sai dai a yau dinnan mai magana da yawun’ yan Kungiyar Brig.Gen Mudoch Agbinibo, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa ‘yan Kungiyar bazasuyi sulhu da gwamnatin ba.
Bamu shirya yin sulhu da kowa ba.. Kuma yaki da gwamnati da fasa bututun mai yanzu muka fara, ba gudu ba ja da baya.