Nijeriya Da Rasha Sun Kulla Yarjejeniyar Aiki Tare A Bangaren Ayyukan Soji


 

4bkbace92e5f8ehflg_800c450

Nijeriya da kasar Rasha sun cimma wata yarjejeniya ta aiki tare a fagen ayyukan sojoji a tsakaninsu da nufin kara karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriyan (NAN) ya jiyo karamar minista a Ma’aikatar cikin gidan Nijeriyan Khadijah Abba-Ibrahim tana cewa gwamnatocin Nijeriya da Rasha suna ci gaba da tattaunawa kan wasu yarjejeniyoyin guda biyu da suka shafi ayyukan soji, wanda ake sa ran nan ba da jimawa za a sanya musu hannu.

Karamar ministar ta kara da cewa yarjejeniyar aiki taren ta kumshi ba da horo da sayen kayayyakin ayyukan soji na zamani da ake bukata kuma a farashi mai rahusa.

Baya ga harkokin soji, har ila yau kasashe biyun kuma suna ci gaba da tattaunawa kan harkokin noma da yadda manoman Nijeriya za su amfana da wannan yarjejeniyar.

Tattaunawa don cimma yarjejeniyar dai ta zo ne a daidai lokacin da wata tawagar jami’an kasar Rashan karkashin jagorancin Dianov Yurievich, daya daga cikin manyan jami’an diplomasiyyar kasar Rashan.

You may also like