Nijeriya Ta Shiga jerin Kasashen Da Suka Daina Shigo Da Man Diesel Daga TuraiKasashe biyar a yammacin Afirka sun yanke shawarar daina shigo da man diesel mara tsafta daga Turai, a cewar hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da muhalli.
Wani rahoto da kungiyar masu fafutuka ta Public Eye ta fitar a watan Satumba ya yi zargin cewa kamfanonin Turai suna fitar da man diesel mai dauke da sinadarin Sulphur ko farar wuta ta hanyar amfani da raunanan dokokin dake yammacin Afirka.

Hukumar ta ce kasashen Najeriya da Benin da Togo da Ghana da kuma Ivory Coast sun amince da matakin. Ta kara da cewa matakin zai taimaka wa mutane sama da miliyan 250 su rika shakar tsaftataciyar iska kuma mara hadari.
Hukumar ta ambato Amina Mohammed, ministar muhalli ta Najeriya tana cewa:

“A tsawon shekara 20 Najeriya ta kasa magance matsalar gurbatar yanayi da motoci ke haifarwa saboda man diesel mara kyau da kasar ke shigowa da shi. A yau za mu dauki wani muhimmin mataki – za mu takaita sinadarin Sulphur a cikin man diesel daga 3000 a kowane miliyan daya zuwa 50 a kowane miliyan daya na yawan sinadarin. 

Yin hakan zai tsaftace iskar da ake shaka a biranenmu kuma zai taimaka mana wajen kafa wata ka’ida da ya kamata ace motocin zamani suna amfani da ita”.

You may also like