Nijeriya Ta Yanke Huldar Jakadanci Da Kasar Taiwan, Ta Zabi China


 

A jiya Laraba, gwamnatin Tarayya ta yanke huldar jakadancin da kasar Taiwan inda ta rufe ofishin jakadancin kasar da ke babban birnin tarayya Abuja, ta kuma jaddada goyon bayanta ga Kasar China a matsayin kasa daya.

Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama shi ya bayyna haka yayin da yake amsa tambayoyi a wani taron manema labarai da ya yi tare da Ministan Harkokin waje na kasar China.

Mista Inyeama ya ce Nijeriya ta yanke shawarar marawa China baya wadda ke ikirarin cewa kasar Taiwan na karkashin mulkinta.

Ya ce har yanzu kasashen duniya ba su amince da Taiwan a matsayin ‘yantacciyar kasa ba a karkashin dokokin kasa da kasa.

Ya kara da cewa, kama daga yanzu, kasar ta Taiwan ba za ta samu wata wulda da Nijeriya ba irin ta jakadanci, sai dai, wakilan kasar za su iya gudanar da kasuwancin su ba matsala. A don haka ne ya ce sun umarci jakadan kasar Taiwan din da su mayar da ofishin su jahar Lagos.

You may also like