
Asalin hoton, Reuters
Rahotanni sun ce Chelsea ta kamalla ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan RB Leipzig da Faransa Christopher Nkunku kuma ɗan wasan mai shekara 25 zai koma can a hukumance a watan Yulin 2023. (Fabrizio Romano, Twitter)
Gareth Southgate ya yanke hukuncin zama a matsayin kocin Ingila bayan kashin da Faransa ta ba ƙungiyarsa a wasan daf da na kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya. (Telegraph)
Shi ma Eddie Howe mai shekara 45 ya ce yana so Southgate mai shekara 52 ya ci gaba da zama a matsayin kocin Ingila duk da ce-ce-ku-cen da ake yi kan cewa shugaban Newcastle na son ɗaukarsa. (Chronicle)
Youssoufa Moukoko mai shekara 18 da Liverpool da Manchester United da Chelsea ke hari bai kusa ƙulla yarjejeniya ba da Borussia Dortmund, kamar yadda wakilin ɗan wasan gaban Jamus ɗin ya tabbatar. (Sky Germany via Liverpool Echo)
Shugaban Angers Said Chabane ya ce kulob din na shirin rabuwa da ɗan wasan Morocco Azzedine Ounahi mai shekara 22 a watan Janairu sakamakon Leicester da Leeds da West Ham na neman ɗan wasan. (Talksport)
A kullum Liverpool na samun ƙarin ƙwarin gwiwa kan cewa su za su yi nasara a neman ɗan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jude Bellingham mai shekara 19. Mirror)
Chelsea na shirin ƙara matsa lamba kan Real Madrid a gwagwarmayar da ake yi ta sayen ɗan wasan RB Leipzig da Croatia Josko Gvardiol mai shekara 20 ta hanyar ƙoƙarin ɗaukarsa a watan Janairu. (Mirror)
Newcastle na daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke neman ɗan wasan gaban Georgia Khivicha Kvaratskhelia mai shekara 21 amma Napoli ba ta son sayar da shi kan farashin fam miliyan 50 kamar yadda aka ruwaito. (90min)
Akwai yiwuwar golan Manchester United da Sifaniya David de Gea mai shekara 32 zai bar Old Trafford a kyauta a kaka mai zuwa sakamakon kulob ɗin bai amince da tsawaita kwantiraginsa ba na tsawon watanni 12. (Sky Germany via Sun)
Ɗan wasan tsakiyar Amurka Christian Pulisic mai shekara 24 ya ce “abubuwa na sauyawa cikin gaggawa kuma komai kan iya faruwa” bayan da aka alaƙanta shi da komawa Manchester United daga Chelsea. (Indirect Podcast via Metro)