Nmandi Kanu Ba Ya Cikin Manyan Mutane   A Yankin Kudu Maso Gabas -Fadar Shugaban Kasa Fadar Shugaban kasa tace bata dauki Nmandi Kanu jagoran kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biyafara a matsayin daya daga cikin dattijai da suka fito daga yankin kudu maso gabas. 

  Baba Femi Ojudu mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin siyasa ya bayyana haka, a matsayin dalilin da yasa ba a gayyaci Nmandi Kanu ba,a tattaunawar da Mukaddashin Shugaban kasa yayi da manyan mutanen da suka fito daga yankin na kudu maso gabas. 

   ” Eh muna neman shugabannin mutane ne, masu tunani, mu bamu dauke shi a matsayin haka ba.watakila dama zata zo anan gaba daza a iya tattaunawa dashi ,” Ojudu yace. 

” Abinda mukayi shine dubo mutane da suke da fada aji a cikin al’umma, ko ta bangaren addini, sarautar gargajiya, Siyasa da kuma harkokin mulki, wadannan sune mutanen da muka kawo domin mu tattauna dasu.”

Yace a zaman da sukayi da shugabannin yankin babu wanda yakawo maganar Biyafara ko kuma batun yin kuriar raba gardama. 

Ojudu yace cigaba da cewa shugabannin yankin na kudu maso gabas sun yarda cewa Najeriya taci gaba da zama kasa daya. 

You may also like