Nmandi Kanu Ya Fasa Ganawa Da Gwamanonin Yankin Kudu Maso Gabas


Nmandi Kanu jagoran kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra ya  janye daga ganarwa da aka shirya zai yi  da kungiyar gwamanonin yankin kudu maso gabas. 

 A baya dai Kanu ya gana da gwamanonin a ranar 30 ga watan Agusta inda suka tattauna batun fafutukar kafa kasar Biafra da kungiyar IPOB keyi.

 Duka bangarorin biyu sun amince su sake tattaunawa akan batun a taron da aka shirya gudanarwa gobe Juma’a a Enugu.

Amma a wata sanarwa da yafitar mai dauke da sa hannunsa Kanu yayi zargin cewa sojoji dake jihar za suyi kokarin kashe shi akan hanyarsa ta zuwa wurin taron.

Ya kuma ce yanzu hankalin kungiyar ya karkata ne wajen kula da mutanen da suka samu raunuka a rikicin da yafaru tsakanin magoya bayan kungiyar da sojoji a garin Aba.

You may also like