NNPC ya dora alhakin karancin man fetur kan dillalai


Kamfanin mai na kasa NNPC ya dora alhakin karancin mai da ake samu a faɗin kasarnan kan dillalan mai.
Maikanti Baru, shugaban kamfanin shine ya bayyana haka  ta bakin mai magana da yawun kamfanin, Ndu Ughamadu cikin wata sanarwa da ya fitar.

Inda yake tabbatar da cewa za a kawo karshen matsalar cikin makon da muke ciki. Baru ya gargadi dillalan man fetur akan boye man inda yace duk gidan man da aka samu da laifin boye man to za a rabar da man ga baki daya kyauta ga masu ababen hawa.

Ya kuma ce wani abun da ya sake ta’azzara matsalar man shine zargin da ake cewa za kara farashin man.

“Amma cikin gaggawa muka shiga aiki ka’in dana’in ta hanyar rubanya abin da muke samarwa a kasa baki daya dai-dai lokaci da jita-jitar ta fara cika gari.muna da mai da zai wadaci kasarnan har tsawon kwanaki 30,” ya ce.

 “A binda ake bukatar samarwa a kullum bai wuce motoci 700 ba hakan yayi dai-dai da lita miliyan 27 zuwa 30.”

Ya kara da cewa kamfanin ya rubanya  yawan man da yake samarwa a kowace rana daga motoci 700 kimanin lita miliyan 27 – 30 ya zuwa lita miliyan 80 a kowacce rana tun lokacin da aka lura da matsalar ƙarancin man.

You may also like