NNPC ya gyara bututun iskar gas wanda ya jawo raguwar wutar lantarki da ake samarwa a ƙasa baki ɗaya


Kamfanin NNPC yace an samu nasarar gyara bututun iskar gas da aka fi sani da bututun Escravos-Lagos  dake dauko iskar  gas daga Escravos a yankin Neja Delta zuwa Lagos. Wanda ya kone sanadiyar wutar daji.

Ndu Ughamadu, mai magana da yawun kamfanin shine ya sanar da haka inda yace tuni aka cigaba da turo iskar gas a bututun domin amfanin abokan cinikayyar kamfanin ciki har da wasu tashoshin samar da wutar lantarki.

A ranar 2 ga watan Janairu wani bangare na bututun dake Abakila a jihar Ondo ya kama da wuta sanadiyar wutar daji.

Lamarin da yafaru ya shafi samar da gas a jihohin Ondo, Ogun da kuma Lagos tare da rufe wasu tashoshin samar da wutar lantarki.

Lamarin dai ya haifar da raguwar wutar lantarki da ake samarwa abin da ya jawo ƙarancin lantarki a duk fadin kasa baki ɗaya.

You may also like