NNPP ta ce ko dar ba ta yi ba kan zuwa kotu a Kano



Zababben gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, ABBA MEDIA FACEBOOK

A Najeriya, jam’iyyar NNPP a jihar Kano da ke arewacin kasar, ta mayar wa APC mai barin gado martani game da kiraye-kirayen da take yi cewa hukumar zabe ta sake nazari kan sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ya bai wa Abba Kabir Yusuf (Gida-gida) nasara a zaben da aka yi da ya ba shi nasara

APC dai ta ce ba ta amince da sakamakon zaben ba, kuma za ta garzaya kotu don ƙalubalantar sa.

To, sai dai shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Umar Haruna Doguwa ya ce duk masu bai wa Dr Nasiru Yusuf Gawuna shawarar ya je kotu to kuwa so suke ya yi biyu babu.

A hirarsa da wakilin BBC a jihar Kano, Doguwa ya ce ko a jikinsu indai kan batun garzayawa kotu ne, ”Wallahi ko gezau ba mu yi ba, aje kotun mun tabbatar mu na da nasara an yi sahihin zabe, dan haka ba za mu hana kowa zuwa kotu ba.”



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like