NTA Jos Ta Gudanar Da Muhadarar Azumin RamadanA karo na 8 a jere, cibiyar watsa shirye shiryen kasa ta NTA Jos ta gabatar da Muhadarar Ramadan, wacce ta mayar da hankali kan kula da tarbiyya da harkokin iyali bisa koyarwar addinin Musulunci. 

Shugaban tashar Nuruddeen Adesina Idris ya ja hankalin al’ummar Musulmi su ba da gudunmawa ga cigaban harkokin addinin Musulunci tare da tsare kima da mutuncin Musulmi a ko’ina a suke. 

Ya bukaci Musulmi a jihar Filato su rika hada kai da tashar domin gabatar da shirye shiryen addini da ilimantarwa, ta yadda sauran al’umma za su amfana. 

Bako mai jawabi a taron Ustaz Muhammad Hashir Sa’id ya gabatar da lucca wacce ta yi nazarin taken taron, inda a ciki ya karfafa gwiwar iyaye su kula sauke hakkokin iyalin da Allah ya ba su amanar rikewa. 
Malamin ya kuma soki wasu iyaye dake sarayar da tarbiyyar yaran su, suna kai su yawon almajiranci, inda za su rika gararamba a titi, babu kyakkyawar Kulawa. 
Shugaban taron wanda ya taba rike kantoman mulkin soja a jihar Katsina, AIG Hamisu Ali Jos shi ma ya bayyana takaicin sa dangane da lalacewar rayuwa. 

You may also like