A birnin Montreal na kasar Kanada,wasu masu kyamar Islama sun manna wata takarda da ke kunshe kalaman nuna kyama a katangar wani Masallaci.
Limamin masallacin Dorval malam Mehmet Değer ya ce wasu matasa 4 ne suka manna wannan takardar a abakin kofar masallacin.
Değer ya kara da cewa ko shakka babu,wadannan matasan karnukan wasu masu kyamar Islama ne,wadanda ke bakin cikin ganin dukkaninmu mu rayu a cikin kwanciyar hankali.
‘Yan sandan Montreal,sun isa wurin ibadar,inda suka dauki alamomin da hannayen masu laifin suka bari a jikin takardar da suka makala,tare da bincikar hotunan da kemarar wannan masallacin ta dauka.