
Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon Liverpool, Darwin Nunez ba zai buga wa tawagar Uruguay wasannin sada zumunta ba, sakamakon raunin da ya ji.
Tun farko kasar ta bayyana dan wasan cikin wadanda za su buga mata fafatawar da za ta yi da Japan da kuma Korea ta Kudu.
Sai dai jinyar da zai yi ba zai buga wasan sada zumuntar da Uruguay za ta kara da Japan ranar 24 ga watan Maris da Korea ta Kudu kwana hudu tsakani ba.
Nunez ya bukaci Likitoci su duba shi a Ingila, domin ya yi jinya a Liverpool, mai buga gasar Premier League.
Liverpool ba ta fayyace girman raunin da dan kwallon ya ji ba kawo yanzu, balle a fayyace lokacin da zai yi zaman jinya.
Nunez ya ji rauni a wasa da Real Madrid a Champions League ranar Laraba, inda kungiyar Sifaniya ta kai quarter finals da cin 6-2 gida da waje.
Tuni Uruguay ta maye gurbin Nunez da Jonathan Rodriguez, mai shekara 29.