NURTW Na Kokarin Shawo Kan Rikicin Shugabancin Da Ya Barke A KungiyarShugaban Kungiyar Amintattu, Najim Usman Yasin ya bayyana hakan ne a wani taro da suka yi a Abuja.

Dattawan kungiyar direbobi ta Najeriya NURTW sun ba da tabbacin sabon yunkuri don warware dambarwar shugabanci a kungiyar.

Sassa biyu na kungiyar da ke hamayya da juna sun yi arangama a helkwatar kungiyar a Abuja a baya-bayan nan.

Taron kungiyar NURTW

Taron kungiyar NURTW

Arangamar wacce ta hada da amfani da makamai ta yi sanadiyyar asarar ran mutum daya da raunata wasu mutum hudu.

Daya daga cikin dattawan Kungiyar Suleiman Danzaki ya ce ya fi kowa dadewa a cikin kungiyar kuma babu wanda ya girme shi a halin yanzu.

Ya kara da cewa duk sa’o’insa a kungiyar wadanda suka yi aiki tare sun riga mu gidan gaskiya, amma bai taba ganin fitina irin wannan ba.

Taron kungiyar NURTW

Taron kungiyar NURTW

Ya kara da cewa, abin da ma ya fi ba shi mamaki shi ne cewa mutane biyu da ke takaddamar, Tajudeen Ibikunle Baruwa da Tajudeen Agbede dukkan su daga kudu maso yamma suke inda aka warewa shugabanci kungiyar a wannan karo, amma kuma suke rigima da junan su

Danzaki ya ce har yanzu wadanda ‘yan sanda suka kama bayan rikicin da mambobin matasa suka haddasa, na kulle, duk da labarin sako wasu da ke mara baya ga wani bangare.

Wannan bayani ya dan saba daga bayanin Shugaban Kwamitin Amintattu na Kungiyar Najeem Usman Yasin wanda ya nemi ya sakaya labarin fito na fito da aka samu.

Taron kungiyar NURTW

Taron kungiyar NURTW

Najeem ya ce an amince za a ga gudanar da sabon zabe ranar 5 ga watan gobe inda kowacce shiyyar siyasa 6 ta Najeriya za ta turo mutum 3.

Shi kuwa Shugaban da ya samu turjiya wajen darewa madafun iko Ibikunle Baruwa ya ce ba gudu ba ja da baya kan tabbatar masa da mukamin, kuma in wani na da korafi ya garzaya kotu, maimakon ta da fitina.

An kammala taro a ofishin kungiyar da ke unguwan Garki a Abuja lami lafiya.

Saurari rahoton:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like