Obama Ya Caccaki Trump Kan Hana Musulmi Shiga AmurkaTsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya caccaki shugaban Amurka Donald Trump kan mataki da ya dauka kan hana musulmai ‘yan wasu kasa shiga Amurka.
Sanarwar da ta fito daga mai magana da yawun Obama, Kevin Lewis ya ce tsohon shugaban kasan ya ji ɗadin zanga-zanga da ake yi don tilasta ma Trump ya janye matakin da ya dauka.

Kevin ya kara da cewa Obama yana kyamar nunawa mutane wariya saboda addninsu. A cewarsa zanga zanga da ake yi ya nanuna cewa Amurkawa ba za su bari a gurbata mulkin demokradiyya ba.
Saidai jami’an fadar ‘White House’ sun ce duk wanda yake kyamar wanan mataki ya yi duk abunda ya ga dama.

You may also like