Obama ya jagoranci bude wani gidan tarihi na bakar fata a birnin Washington


Shugaba Barack Obama a karo na farko ya jagoranci bikin bude wani gidan tarihi na bakar fata a birni Washington. Gidan dake dauke da tarihin bakar fata a Amurka, an dai bayyana cewa a wannan wuri an ajiye kayyakin tarihi dake nuna jarumtakar bakar fata kama daga lokutan bauta na jahiliya zuwa lokutan da aka soma samun bakaken fata a harakokin yau da kullum a kasar ta Amurka.
Ana danganta bude wannan katafaren wuri da Shugaba Obama yayi kafin sauka daga mukaminsa na Shugaban kasar Amurka a watan janairu shekarar badi a matsayin nasara.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like